Tsallaka zuwa abun ciki
Sunni Islam Shiriya, kayan ibada da sahihan madogarai

Sura 95 · Makkiyya · 8 Ayoyi

Sura At-Tin

Ɓaure

سورة التين
Saurara a jere

بِسْمِ ٱللَّهِ ٱلرَّحْمَٰنِ ٱلرَّحِيمِ

  1. 1

    وَٱلتِّينِ وَٱلزَّيْتُونِ

    Inã rantsuwa da Attinu da Azzaitũn.

  2. 2

    وَطُورِ سِينِينَ

    Da Dũr Sĩnĩna.

  3. 3

    وَهَٰذَا ٱلْبَلَدِ ٱلْأَمِينِ

    Da wannan gari amintacce.

  4. 4

    لَقَدْ خَلَقْنَا ٱلْإِنسَٰنَ فِىٓ أَحْسَنِ تَقْوِيمٍۢ

    Lalle ne, Mun halitta mutum a cikin mafi kyawon tsayuwa.

  5. 5

    ثُمَّ رَدَدْنَٰهُ أَسْفَلَ سَٰفِلِينَ

    Sa'an nan, Muka mayar da shi mafi ƙasƙantar masu rauni

  6. 6

    إِلَّا ٱلَّذِينَ ءَامَنُوا۟ وَعَمِلُوا۟ ٱلصَّٰلِحَٰتِ فَلَهُمْ أَجْرٌ غَيْرُ مَمْنُونٍۢ

    Face waɗanda suka yi imani, kuma suka aikata ayyukan ƙwarai, saboda haka suna da sakamako wanda bã ya yankewa.

  7. 7

    فَمَا يُكَذِّبُكَ بَعْدُ بِٱلدِّينِ

    To, bãyan haka mẽ ya sanya ka ka ƙaryata sakamako (wanda za a yi a bãyan Tãshin ¡iyãma)?

  8. 8

    أَلَيْسَ ٱللَّهُ بِأَحْكَمِ ٱلْحَٰكِمِينَ

    Ashe Allah bã Shi ne Mafi mãsu hukunci kyãwon hukunci ba?

Larabci: rubutun Uthmani na Tanzil. Fassara da sauti ta hanyar Al Quran Cloud / Islamic Network kyauta. Tafsiri ta Tafsir API na buɗaɗɗen tushe.